Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cibiyar kasuwancin Najeriya zata bude kasuwanni yayin da ake yaki da COVID-19
2020-05-19 10:23:56        cri
Gwamnan jahar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya ce, ana duba yiwuwar bude wasu daga cikin muhimman bangarorin kasuwanci a cibiyar tattalin arzikin Najeriyar wacce ta kasance wurin da annobar COVID-19 tafi kamari a kasar bayan da aka yi nazarin dacewar yin hakan.

A taron manema labarai da gwamnan yayi a ranar Lahadi, ya ce, yunkurin bude kasuwannin za'a gudanar da shi ne sannu a hankali babu gaugawa.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu yace, gwamnatin jahar zata bullo da wani tsarin yin rajista a matsayin wasu dabarun da zasu taimaka wajen duba yanayin fannonin kasuwanci da suka fi dacewa a bude tare da aiwatar da shirin bibiyar fannonin a cikin wasu kwanaki masu zuwa.

A cewar gwamnan, jami'ai daga hukumomin kula da tsaro da hukumar kare muhalli ta jahar Legas zasu dinga ziyartar gidajen sayar da abinci, kamfanoni, da wuraren ibadu domin duba yanayin ingancinsu. Ya kara da cewa, bisa la'akari da girman kasuwancin jahar da kuma fannonin kasuwanci da suka cancanci a bude su a jahar Legas, gwamnati ba zata cigaba da killace mutane a gida da dakatar da kasuwancin na dindindin ba.

Sai dai kuma, Sanwo-Olu, yayi gargadin cewa, kada a yiwa bude kasuwanci gurguwar fahimta kasancewa matakin bai bayar da lasisin bude dukkan kasuwanci ba.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China