Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An halaka mayakan BH da dama yayin wasu ayyukan soji a Nijeriya
2020-05-16 16:25:30        cri
Ma'aikatar tsaro ta Nijeriya, ta ce an kashe mayakan Boko Haram da dama a yankin arewa maso gabashin kasar, yayin wasu ayyukan soji da aka kaddamar a baya-bayan nan.

Kakakin ma'aikatar, John Enenche, ya ce rundunar Operation Lafiya dole, da aka kafa domin fatattakar BH daga yankin, ta yi nasarar kai hare-haren kan maboyar mayakan kungiyar daga ranar 8 ga wata, lamarin da ya kai ga kashe 61 daga cikinsu.

Baya ga haka, wasu mayaka 11 sun mika wuya ga sojojin kasar yayin da sojojin ke tsaka da kaddamar da hare-hare a yankin na arewa maso gabas.

Mambobin kungiyar ISWAP dake taimakawa BH ne suka mika wuya ga sojojin, ranar 11 ga wata a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China