Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta tsawaita sassauta dokar kulle na mako 2 don yaki da COVID-19
2020-05-19 11:29:24        cri

Gwamnatin Najeriya a ranar Litinin ta sanar da tsawaita sassauta dokar zaman gida da mako biyu, a matsayin matakin dakile yaduwar annobar COVID-19 a kasar.

Sakataren gwamnatin kasar, Boss Mustapha, yace duk da irin nasarorin da aka samu a yaki da cutar a halin yanzu, Najeriya ba zata yi cikakken bude kasuwancinta ba.

Mustapha ya fadawa taron manema labarai a Abuja cewa, matakan da aka dauka na sassauta dokar kullen kan wasu jerin bangarorin da aka amince dasu a zagayen farko na dokar su kadai ne zasu cigaba da zama a bude, kuma za'a cigaba da aiwatar da dokar sassaucin ne a duk fadin kasar har na tsawon makonni biyu wadda ta fara aiki daga tsakiyar daren ranar 18 ga watan Mayu zuwa ranar 1 ga watan Yuni.

Yace gwamnati ta mayar da hankali kan matakan da ta dauka na baya bayan nan domin kara aikin bincikowa da kula da masu dauke da cutar da dakile bazuwar annobar a tsakanin al'umma.

Kimanin mutane 5,959 ne suka kamu da cutar COVID-19 a kasar mafi yawan jama'a a Afrika, sai mutane 182 da cutar ta kashe, yayin da mutane 1,594 sun warke daga cutar ya zuwa ranar Litinin, kamar yadda cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya ta sanar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China