2020-05-16 16:22:21 cri |
Darakta janar na cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta kasar, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana yayin wani taron manema labarai da ya gudana jiya a birnin Abuja cewa, makarin hanci da baki karin mataki ne na kandagarki, kuma bai kamata a maimaita amfani da shi ko kuma mutane biyu su yi amfani da guda daya ba.
Ya ce sanya makarin hanci da baki yadda ya kamata, zai iya kare yaduwar COVID-19.
A watan da ya gabata ne hukumomi a kasar suka tilasta sanya makarin baki da hanci domin dakile yaduwar kwayar cutar. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China