Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Buhari ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa
2020-05-14 10:31:09        cri
A ranar Laraba shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar, makonni bayan rasuwar babban jami'in fadar shugaban kasar wanda ya mutu a sanadiyyar annobar COVID-19.

Sabon jami'in mai taimakawa shugaban kasa, Ibrahim Gambari, ya samu tarba daga manyan jami'an fadar shugaban kasar dake Villa, a Abuja, gabanin fara taron majalisar gudanarwar kasar wanda shugaban kasar Muhammadu Buhari ke jagoranta ta kafar bidiyo.

A matsayinsa na gogaggen masanin diflomasiyya, Gambari yana da matukar kwarewar aiki, da ilmi mai zurfi a fannin koyarwa, kana da kwarewa a fannin mulki da dangantakar kasa da kasa, baya ga kasancewarsa a matsayin wanda ya taba rike mukamin babban jami'i karkashin sakatare janar na MDD sannan mashawarci na musamman ga babban jami'in MDD mai kula da al'amurran Afrika tsakanin 1999 da 2005.

A matsayinsa na sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Gambari zai shugabanci mukamin gwamnati mai girma wanda zai dinga samun umarni kai tsaye daga shugaban kasar Najeriya.

Tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar, Abba Kyari, ya mutu a ranar 17 ga watan Afrilu a jihar Legas bayan ya sha fama da jinyar cutar COVID-19.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China