2020-05-24 16:07:15 cri |
John Enenche, mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikewa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce an kashe 'yan bindigar ne a yayin wasu hare hare ta jiragen sama da rundunar musamman ta sojojin Najeriya ta Operation Hadarin Daji suka kaddamar a yankuna masu yawa a jahohin biyu tsakanin ranar Laraba zuwa Juma'a.
A cewar kakakin sojojin, hare haren ta sama na daga cikin sabbin munanan hare haren da sojojin suka kaddamar a shiyyar arewa maso yammacin Najeriyar da nufin murkushe ayyukan mayakan 'yan bindigar da sauran bata gari a yankunan.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China