Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin jakadancin Sin dake Birtaniya ya maida martani ga aikawa firaminisan kasar Birtaniya wasika da wasu tsoffin jami'an diplomasiyya 7 suka yi
2020-06-03 10:57:27        cri

Jiya Talata, kakakin ofishin jakadancin kasar Sin dake Birtaniya ya maida martani a gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana game da batun tsoffin jami'an diplomasiyya guda 7 da suka aikawa firaministan kasar Boris Johnson wasika dangane da kasar Sin.

Kakakin ya ce, kasar Sin na bayyana matukar rashin jin dadi saboda ganin wadannan tsoffin jami'an sun tsoma baki kan kafa dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong, yana mai cewa bai kamata a yi shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar Sin ba ko kadan.

Ya kara da cewa, da farko, kasashen waje ba su da ikon tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong. Na biyu kuwa, kafa dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong iko ne na kasar Sin, kuma nauyi ne dake wuyan gwamnatin tsakiya na kula da harkokin al'umma. Na uku kuma, ya ce babu gaskiya dangane da ikirarin da ake cewa, dokar ta sabawa hadaddiyar sanarwar dake tsakanin Sin da Birtaniya. Gwamnatocin kasashen biyu sun ba da hadaddiyar sanarwa a watan Disamban shekarar 1984, da zummar warware batun komawar yankin Hong Kong hannun babban yankin kasar Sin. Iko da kuma nauyin dake da nasaba da Birtaniya sun kare bayan ranar 1 ga watan Yulin shekarar 1997, lokacin da yankin Hong Kong ya dawo hannun babban yankin kasar Sin. Na karshe, yankin ya shiga karkashin aikin tsaron kasar, wanda zai amfana wajen aiwatar da tsarin "Kasa daya mai tsarin mulki biyu" da kiyaye iko da 'yancin mazauna Hong Kong. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China