Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babbar jagorar yankin Hong Kong ta goyi bayan gyaran fuska ga dokokin tsaron kasa masu nasaba da yankin
2020-05-22 20:29:24        cri
Babbar jagorar yankin Hong Kong Carrie Lam, ta bayyana goyon bayanta ga kudurin gyaran fuska ga dokokin tsaron kasa, masu nasaba da yankin na Hong Kong mai cin gashin kansa. A Juma'ar nan ne dai Carrie Lam ta nuna amincewa da kafawa, tare da inganta tsarin shari'a, da aiwatar da shi a yankin, matakin da a cewarta, zai bunkasa tsaron kasa yadda ya kamata.

Cikin wata sanarwa, Carrie Lam ta kara da cewa, kare martabar ikon mulki, da tsaron kasa, da dora muhimmanci kan bukatun tsarin mulkin yankin na Hong Kong, nauyi ne dake wuyan mahukuntan yankin, abu ne kuma da daukacin al'ummar yankin ke maida hankali a kansa.

Daga nan sai ya jaddada kasancewar yankin Hong Kong, wani bangare da har abada zai kasance hade da kasar Sin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China