Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu kishin kasar Sin a Hong Kong sun kaddamar da "babban kawancen sake farfado da Hong Kong"
2020-05-05 21:01:22        cri
Da safiyar yau Talata ne wasu mutane 1545 daga bangarori daban-daban a yankin Hong Kong na kasar Sin, suka kaddamar da babban kawancen sake farfado da yankin na Hong Kong, da zummar hada kawunan bangarori daban-daban domin nemowa yankin mafita.

Mataimakan shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, Mista Tung Chee-hwa, da Mista Leung Chun-ying sun zama wadanda suka bada shawarar kafa kawancen, sa'annan memba a kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama'ar kasar, Mista Tam Yiu-chung, ya zama babban sakataren kawancen, ita kuma mataimakiyar daraktan kwamitin tsara babbar doka ta Hong Kong, a kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Madam Tam Wai-chu na daya daga cikin mataimakan babban sakataren kawancen.

A wajen taron manema labarai da aka yi, kawancen sake farfado da Hong Kong ya fitar da wata sanarwa, inda ya yi kira a tsaya kan muhimmiyar manufar "kasancewar kasa daya amma tsarin mulki biyu", da himmatuwa wajen sake bunkasa yankin.

Kawancen na ganin cewa, a halin yanzu akwai kamfanoni manya da kanana da dama, wadanda suke cikin halin rai kwaikwai mutu kwaikwai, don haka ya zama dole a bunkasa tattalin arziki, da tabbatar da isassun guraban ayyukan yi, da kuma sake maido da zaman doka da oda a Hong Kong. Har wa yau, an yi kira ga bangarori daban-daban, da mutanen da suke da mabambantan ra'ayoyin siyasa, su zama tsintsiya madaurinki daya, domin nemawa Hong Kong mafita.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China