2020-05-31 21:08:29 cri |
Bayanin ya ce, bayan da aka samu rikicin gyaran doka a yankin Hong Kong a bara, masu tada rikicin sun kai hare-hare ga 'yan sanda, da yin garkuwa da fararen hula ba bisa doka ba, da kai hare-hare ga gine-ginen gwamnatin yankin da sauransu, hakan ya sa yankin ya samu tabarbarewar tattalin arziki sosai. A cikin dogon lokaci, an kasa samun tabbaci kan kiyaye tsaron kasa a yankin Hong Kong, don haka an samu tada zaune tsaye a yankin, har ma an kawo illa ga tsaron kasar Sin. Tilas ne a yi amfani da dokar kiyaye tsaron kasa ta yankin don daidaita matsalar yankin. A kwanakin baya, an zartas da dokar kiyaye tsaron kasa ta yankin a gun taron wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, wadda jama'ar kasar Sin ciki har da mazauna yankin Hong Kong suka nuna goyon baya gare ta.
Bayanin ya kara da cewa, dokar ta shafi ayyukan kawo illa ga tsaron kasar Sin ciki har da ayyukan 'yan aware, da juyin juya hali, ayyukan ta'addanci, da tsoma baki kan harkokin cikin gida da kasashen waje suka yi. Duk mutumin da bai aikata wani laifin saba doka ba, to babu damuwa zai iya zaman rayuwarsa a yankin Hong Kong yadda ya kamata. Kafa dokar zata tabbatar da ikon sarrafa harkokin yankin da kansa, da kuma kiyaye yanayin dokoki da kasuwanci a yankin. Zaman lafiya a yankin zai kara kawo kyakkyawar dama ga yankin, kana za a kawo moriya ga mutanen kasa da kasa da suke son yin aiki ko zuba jari ko yin rayuwa a yankin. (Zainab)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China