Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangaren yawon shakatawa a HK na fama da kalubale duk da hutun ranar maaikata da aka yi
2020-05-04 10:15:59        cri

Bisa alkaluma na baya-bayan nan da sashen kula da shige da fice na gwamnatin Hong Kong ya fitar, yankin ya samu masu shiga 1,528 a ranar farko ta hutun kwanaki 4 da aka yi, inda mazauna yankin suka mamaye kaso 90 bisa 100 na adadin, yayin da yawan masu ziyara daga babban yankin kasar Sin ya sauka zuwa 119.

Domin saukakawa mazauna matsalolin da COVID-19 ta haifar, gwamnatin HK ta kaddamar da zagaye biyu na tallafi da matakan rage radadi da dama, domin taimaka musu tunkarar yanayin da ake ciki.

Ingantattun matakan tunkarar cutar da kokarin da gwamnatin ta yi a fannonin daban-daban, sun ba bangaren na yawon shakatawa kyakkyawan fata.

Sakataren harkokin kudi na gwamnatin HK Paul Chan, ya ce tattalin arzikin yankin na gab da durkushewa, kuma hasashen da za a yi kan ci gaban alkaluman tattalin arziki a cikin rubu'in farko na bana zai fi muni, saboda ci gaba da ake da zanga-zanga da kuma fama da annobar COVID-19.

Ya ce ci gaba da kokarin dakile annobar, tare da fara sassauta matakan kandagarki a bangarori daban-daban, za su taimaka wajen farfado da harkoki, yana mai cewa, yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali na da muhimmanci wajen sake farfado da tattalin arzikin yankin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China