Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin ma'aikatar harkokin wajen Sin dake yankin Hong Kong: Matakan gwamnatin Sin kan 'yan jaridar Amurka sun dace
2020-03-19 13:10:22        cri

A jiya ne ofishin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin dake yankin Hong Kong ya gabatar bayani a shafinsa na yanar gizo, inda ya bayyana cewa, a jiya ne, kungiyar 'yan jaridar kasashen waje da ke yankin Hong Kong wato FCC ta yi kalaman da su dace ba game da matakan da Sin ta dauka don mayar da martani kan yadda Amurka ta kayyade hukumomin 'yan jaridar Sin da ke gudanar da harkokinsu a Amurka, kakakin ofishin ma'aikatar harkokin wajen Sin dake yankin Hong Kong ya nuna rashin jin dadi da kin amincewa da kalaman.

Kakakin ya bayyana cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa 'yan jaridar kasar Amurka da abin ya shafa ba zasu samu damar ci gaba da aiki a matsayin 'yan jarida a daukacin kasar Sin ba, ciki har da yankunan musamman na Hong Kong da Macao. Wannan mataki shine martanin da Sin ta mayar kan yadda Amurka ta dauki irin matakan ga 'yan jaridar kasar Sin, matakan sun dace kuma dalilin faruwar lamarin ba daga bangaren kasar Sin ba ne.

Kakakin ya jaddada cewa, yankin Hong Kong yanki ne na kasar Sin. Zargin da aka yiwa gwamnatin kasar Sin wai ta tsoma baki kan harkokin yankin Hong Kong bashi da tushe. Sin ta ki amincewa da sassan kasashen waje da suka yi amfani da 'yancinsu na watsa labaru don tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin da kuma harkokin yankin Hong Kong. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China