Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'ar MDD ta zayyana rashin daidaiton tasirin COVID-19 kan kananan kabilu
2020-06-03 10:25:55        cri

Babbar kwamishinar hukumar kare hakkin bil-Adam ta MDD Michelle Bachelet, ta bayyana cewa, rashin daidaito da barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta haifar, na kara ta'azzara zanga-zanga a daruruwan birane a kasar Amurka.

Jami'ar wadda ta bayyana haka cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ta ce kwayar cutar, tana kara fito da rashin daidaito da aka dade ana watsi da su. Yanzu haka, boren da ya barke a kasar Amurka, biyo bayan mutuwar George Floyd, ya kara fito da rashin jituwar dake tsakanin 'yan sandar kasar da wadanda ba fararen fata ba, baya ga rashin daidaito a fannonin kiwon lafiya, da ilimi, da aikin yi da nuwa wariya a fanni annoba.

A cewarta, da alamun tasirin da annobar COVID-19 ta yi kan 'yan asalin Afirka da kananan kabilu a wasu kasashe ya fi muni.

Ta ce, rahotanni sun nuna cewa, yawan Amurkawa 'yan asalin Afirka da cutar ta halaka a kasar Amurka, sun fi na sauran kungiyoyin kabilun kasar yawa har fiye da sau biyu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China