2020-05-28 11:02:36 cri |
Jiya Laraba, cikin taron "kare tsaron fararen hula cikin rikice-rikice" da kwamitin sulhu na MDD ya kira ta kafar bidiyo, Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana cewa, bai kamata a siyasantar da batun kare fararen hula ba, bai dace a maida batun kare fararen hula a matsayin hujjar tsoma baki a harkokin cikin gida ko kuma neman sauyin mulki ba. Ya kamata bangarorin da rikicin ya shafa su dauki nauyin kare fararen hula bisa dokar kasa da kasa, musamman ma a fannin kiyaye mata da yara da sauran marasa galihu. Haka kuma, Zhang Jun ya yi kira ga gwamnatocin kasa da kasa su dauki nauyin kare fararen hula yadda ya kamata, da kuma nuna girmamawa kan 'yancin kasar da rikicin ya shafa. (Maryam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China