Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Asusun UNICEF ya bayyana takaici kan hare-haren da aka kai birnin Tripoli
2020-06-02 10:46:25        cri
Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya bayyana takaici dangane da hare-haren da ya yi sanadin mutuwa da raunata wasu fararen hula a Tripoli, babban birnin Libya.

Wata sanarwa da asusun UNICEF ya fitar, ta ce sun kadu da asarar rayukan da aka yi a Tripoli, biyo bayan samun rahoton mutuwar mutane 5 da raunatar wasu 12.

Sanarwar ta ce kisa da raunata yara a lokacin yaki, daya ne daga cikin laifukan yaki 6.

Ta kuma bayyana ranar a matsayin ta bakin ciki ga iyalai a Tripoli. Tana mai cewa harin ya kashe tare da raunata yaran dake wasa cikin nishadi. A cewar asusun, yaran kasar ba za su iya zaman jiran zaman lafiya ba domin a yanzu suke bukatarta.

Fararen hula da dama sun mutu yayin da wasu suka jikkata sanadiyyar harin na ranar Lahadi a Tripoli.

Dakarun gwamnatin da MDD ke marawa baya, sun zargi rundunar sojin dake gabashin kasar da kai harin, wanda kawo yanzu, bangaren adawar bai mayar da martani ba.

Duk da kiraye-kirayen da kasashen duniya ke yi na a tsagaita bude wuta, gwamnatin kasar da MDD ke marawa baya, da rundunar sojin dake adawa da ita, na ci gaba da gwabza fada kan neman iko da birnin na Tripoli. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China