Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci Amurka da Birtaniya su daina tsoma baki cikin harkokin yankinta na HK
2020-05-30 17:26:07        cri
Zaunnen wakilin kasar Sin a MDD, Zhang Jun, ya bukaci Amurka da Birtaniya, su daina tsoma baki cikin harkokin yankinta na HK, da daina dabi'ar babakere da neman karawa kansu karfi ta hanyar siyasa, su mayar da hankali kan abun da ya shafe su, maimakon ta da rikici a ko ina.

Zhang Jun, ya kuma yi watsi da ikirarin Birtaniya da Amurka da sauran wasu kasashe suka yi kan HK. Yana mai cewa kasar Sin ba ta amince da furucin mara tushe da kasashen suka yi ba.

Wata sanarwa da tawagar Sin a MDD ta fitar, ta ce Amurka da Birtaniya, sun yi ta tsokacin da bai kamata ba, tare da tsoma baki da neman gudanar da taro ta kafar bidiyo a kwamitin sulhu na MDD, domin wasu bukatunsu na siyasa. Inda ta ce kasar Sin na adawa da matakin nasu, kuma galibin mambobin kwamitin ba su amince da bukatar Amurka ba, domin sun yi amana cewa, batutuwan da suka shafi HK, batu ne na cikin gidan kasar Sin, kuma babu abun da ya hada su da ayyukan kwamitin.

Sanarwar ta ce kwamitin sulhun ya yi watsi da bukatar Amurka da sauran yunkurinta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China