Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta jaddada bukatar kawar da wariya a yaki da COVID-19
2020-05-30 16:38:20        cri
Hukumar kare hakkokin bil adama ta MDD, ta amince da sanarwar shugabar hukumar kan tasirin cutar COVID-19 a kan hakkokin bil adama.

Sanarwar ta jaddada cewa, ba za a iya shawo kan cutar ba, har sai kasashen duniya sun hada kai sun zama tsintsiya madaurinki daya tare da goyon bayan juna da kuma daukar mataki na bai daya, karkashin wata dabara da za ta karbu ga dukkansu da kuma cibiyoyin kasa da kasa masu karfi.

Sanarwar ta jaddada muhimmiyar rawa da tsarin MDD ke takawa wajen shirya ayyukan yaki da dakile yaduwar cutar a duniya da goyon bayan da take ba kasashe mambobinta, tare da yabawa gagarumar rawar da WHO ke takawa.

Wannan shi ne daftari na farko kan tasirin COVID-19 kan hakkokin bil adama da hukumar ta amince da shi, wanda ya samu goyon baya daga kasashe mambobinta da na 'yan kallo a hukumar, tare kuma da bayyana buri na bai daya na al'ummar duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China