Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata karin kasashen Afrika su amsa kiran MDD na tsagaita bude wuta
2020-05-26 10:53:43        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce ya kamata karin kasashen Afrika su amsa kiran MDD dake bukatar tsagaita bude wuta a duniya domin fatattakar cutar COVID-19.

A sakonsa na tunawa da ranar kafa kungiyar tarayyar Afrika AU, wadda aka yi a ranar 25 ga watan Mayun shekarar 1963, Sakatare Janar din ya ce annobar COVID-19 na barazana ga kokarin samun ci gaba, wanda zai ba kasashe damar cimma muradun ci gaba masu dorewa da ajandar ci gaba ta Tarayyar Afrika da ake son cimmawa zuwa shekarar 2063.

Ya ce Tarayyar Afrika ta kafa kwamitin hadin gwiwa domin samar da wata dabara ta bai daya a nahiyar, sannan ta nada wakilai na musammam da za su samo tallafi daga kasa da kasa. Ya kara da cewa, kwamitin tsaro na tarayyar, ya dauki matakan shawo kan tasirin COVID-19 game da aiwatar da wasu muhimman yarjeniyoyin zaman lafiya da na maslaha. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China