Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakatare Janar na MDD ya yi kira da hadin kai a cikin sakonsa na karamar Sallah
2020-05-23 16:10:44        cri
Cikin sakonsa na taya murnar karamar sallah, Sakatare Janar na MDD´╝îAntonio Guterres, ya yi kira da hadin kai da goyon bayan juna yayin da ake fuskantar annobar COVID-19.

Antonio Guterres ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilan kasashe mambobin majalisar daga kungiyar kasashe musulmi, gabanin ranar Sallah da ta fado a gobe Lahadi.

Sakatare Janar din ya ce duniya guda daya ce. Kuma muddun wani bangare na fama da cuta, to ta shafi dukkan bangarori. Yana mai cewa yanzu fiye da ko wane lokaci, dole ne hadin kai da goyon bayan juna su kasance abubuwan mafi muhimmanci.

Ya kuma yi kira da goyon bayan juna domin samun aikawatar da ingantattun ayyukan kare lafiya masu yawa, karkashin hukumar WHO, bisa mayar da hankali kan kasashe maso tasowa da mutane masu rauni. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China