Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi kira da a yi amfani da karin dabaru domin taimakawa duniya farfadowa daga tasirin annobar COVID-19
2020-05-29 12:46:36        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yi kira ga kasashen duniya su yi amfani da karin dabaru, ciki har da duba yuwuwar bada kudaden ajiya na asusun IMF wato Special Drawing Rights, domin taimakawa duniya, musammam matalautan kasashe, farfadowa daga mummunan tasirin annobar COVID-19.

Antonio Guuterres ya bayyana yayin wani taro ta kafar bidiyo kan samar da kudaden raya kasa yayin da ake fama da annobar ta COVID-19 cewa, ana da dabarun inganta samar da kudi a duniya, don haka yake bukatar a yi amfani da su, musammam ba da kudaden ajiya.

Da yake tsokaci kan basussukan da ake bin kasashe, Sakatare Janar din ya ce matsalar tattalin arziki da COVID-19 ta haifar, na barazanar mayar da hannun agogo baya a kasashe masu tasowa.

Ya ce yawan basussuka zai haifar da koma baya ga aikin tunkarar COVID-19 da tarnaki ga samun ci gaba mai dorewa a shekaru da dama masu zuwa. Yana mai cewa, kasashen da annobar ta shafa za su gaza samun damar cimma muradun ci gaba masu dorewa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China