Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala babban taron lafiya na duniya da alkawarin shawo kan COVID-19
2020-05-20 11:20:06        cri

An kammala babban taron majalisar kiwon lafiya ta duniya karo na 73 a jiya Talata, da alkawarin yaki da annobar COVID-19. Taron dai, shi ne irinsa na farko da aka yi ta kafar bidiyo tun bayan kafa hukumar lafiya ta duniya a shekarar 1948.

A jawabinsa na rufe taron, darakta Janar na hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa, hukumarsa za ta yaki annobar da dukkan abun da take da shi.

Kafin rufe taron a jiya, wakilai sun amince da matakin hada kan dukkan kasashen duniya wajen yaki da annobar, wanda mataki ne da daukacin wakilan suka amince da shi, bayan kasashe sama da 130 sun gabatar da kudurin, ciki har da Tarayyar Turai da Rasha da Sin.

Har ila yau, taron ya amince da muhimmiyar rawar da WHO da MDD ke takawa wajen tsara yadda duniya za ta shawo kan annobar COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China