Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen duniya sun dogara da MDD wajen shawo kan kalubalen cutar COVID-19
2020-05-12 10:13:19        cri
Mataimakiyar Sakatare Janar na MDD Amina Mohammed, ta ce mutane da kasashe a ko ina, sun dogara kan MDD fiye da ko yaushe, wajen shawo kan kalubalen annobar COVID-19.

Amina Mohammed ta bayyana haka ne yayin wani taro ta kafar bidiyo na majalisar kula da tattalin arziki da zaman takewa kan "hada hannu: ingantattun hanyoyin tunkarar COVID-19" .

Ta kara da cewa, tun bayan barkewar cutar, MDD ta tashi tsaye ta hannu tawagoginta dake kasashe 131 wajen gaggauta taimakawa hukumomin kasashn duniya shiryawa inganta tsarin kiwon lafiyar al'umma da shirye-shiryen tunkarar cutar.

Jami'ar ta kara da cewa, akwai bukatar sanin abubuwa biyu masu matukar muhimmanci, wato dole ne a gaggauta tunkarar cutar domin kawar da tasirinta, haka kuma tilas ne a taimakawa gwamnatoci da mutane tunkarar cutar ta yadda za a kai ga samun makoma mai dorewa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China