Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin, Japan da Koriya ta Kudu sun yi taron ministocin kiwon lafiya don yaki da cutar COVID-19
2020-05-18 20:03:06        cri
Yayin taron manema labaran da aka yi a yau Litinin, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi bayani kan taron ministocin kiwon lafiya na kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu, game da fuskantar cutar numfashi ta COVID-19, wanda aka yi ta kafar bidiyo a daren ranar 15 ga wata.

Zhao Lijian ya ce a yayin taron, an zartas da wata sanarwar hadin gwiwa. Kuma taron, muhimmin jigo ne na musayar fasahohin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da aka gudanar tsakanin kasashen uku, bayan taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu ta fuskar batun cutar COVID-19, wanda aka yi a watan Maris, da kuma taron shugabanni, da taron ministocin kiwon lafiya da kasashen uku suka yi da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya na ASEAN a watan Afrilu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China