![]() |
|
2020-05-27 10:27:32 cri |
Shugabar kwamitin kafa dokokin yankin Hong Kong ta farko Madam Rita Fan Hsu Lai Tai ta shedawa manema labarai a kwanan baya cewa, 'yan tawaye na tada zaune tsaye a yanki da nufin illata shi. Ta ce dole a dauki matakin da ya dace don kyautata halin karancin doka da shari'a wajen tabbatar da tsaron Hong Kong, ta yadda za a dakile masu tada zaune tsaye a yankin. Ta ce ajandar tattaunawa kan batun Hong Kong cikin taron NPC, abu ne da ya wajaba, wanda kuma ya zo a lokacin da ya dace.
A cewarta, dokar tsaron Hong Kong za ta ba da tabbaci ga tsarin "Kasa daya mai tsarin mulkin biyu" ciki dogon lokaci, kuma za ta tabbatar da zaman rayuwa cikin wadata a yankin. (Amina Xu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China