Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ya yi tsokaci kan zartas da dokar kare hakkin dan adam da demokaradiyyar Hong Kong wanda majalisar dattijan Amurka ta yi
2019-11-20 11:18:39        cri
A ranar 20 ga wata,Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ya yi tsokaci kan zartas da dokar kare hakkin dan adam da demokaradiyyar Hong Kong wanda majalisar dattijan Amurka ta yi.

Geng Shuang ya ce, a ranar 19 ga watan Nuwamba ne, majalisar dattijan Amurka ta yi mahawara tare da amincewa da dokar kare hakkin dan adam da demokaradiyya a Hong Kong. Kasar Sin ta yi Allah wadai da babbar murya kuma tana adawa da wannan doka wanda ya shafi harkokin cikin gidan kasar Sin. Ya ce, yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar Sin ya saba dokokin kasa da kasa kuma ya saba muhimman yarjejeniyoyin dangantakar kasa da kasa.

Cigaban tashe tashen hankula a Hong Kong ya yi matukar illa ga yanayin zaman lafiyar yankin dake bin tsarin "kasa daya amma tsarin mulki biyu". Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin za ta cigaba da goyon bayan gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, don ta gudanar da harkokinta bisa tsarin dokoki, da taimakawa 'yan sandan Hong Kong wajen tabbatar da doka da oda, da kotunan shari'ar Hong Kong don hukunta dukkan wadanda aka samu da laifukan tada rikici bisa abin da doka ta tanada, da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama'a mazauna Hong Kong, domin tabbatar da cigaban zaman lafiya mai dorewa a yankin Hong Kong.

Geng Shuang ya gargadi bangaren Amurka da ta dauki matakan gaggawa wajen kau da dokar da aka zartas. Idan har Amurka ta kuskura ta yi gaban kanta, kasar Sin zata dauki tsauraran matakai domin kare 'yancin kanta, da tsaro, da kuma cigaban kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China