Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ba ta da ikon yin kalaman da ba su dace ba kan harkokin Hongkong, in ji ma'aikatar harkokin wajen Sin
2020-01-08 20:00:08        cri
Yau Laraba, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya sake jaddada cewa, harkokin yankin Hongkong harkokin cikin gida na kasar Sin ne, don haka babu gwamnatocin ketare, ko kungiyoyi ko daidaikun mutane dake da ikon tsoma baki cikin harkokin yankin Hongkong. Geng Shuang ya yi wannan tsokaci ne yayin da yake mayar da martini kan kalaman da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya yi kan batun Hongkong.

Rahotanni na cewa, a ranar 7 ga wata, Mike Pompeo ya bayyana cewa, yana fatan kasar Sin za ta martaba sanarwar hadin gwiwar Sin da Burtaniya, gami da kiyaye 'yancin yankin Hongkong. Dangane da wannan batu, Geng Shuang ya ce, tun bayan da yankin Hongkong ya dawo karkashin ikon kasar Sin, gwamnatin kasar Sin tana tafiyar da harkokin yankin kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa da dokar yankin musamman na Hongkong suka tanada yadda ya kamata, tana kuma kiyaye iko da 'yancin al'ummomin yankin Hongkong bisa doka. Kasar Amurka da sauran kasashen waje ba su da ikon yin sharhi kan sanarwar hadin gwiwar Sin da Burtaniya da kuma tsoma baki cikin harkokin Hongkong.

A taron manema labaran da aka yi a yau, Geng Shuang ya kuma bayyana cewa, muhimmin aikin ofisoshin jakadancin kasar Sin dake kasashen ketare shi ne kiyaye muradun kasa da al'umma, raya dangantakar abokantaka a tsakanin kasar Sin da kasashen ketare, a maimakon yin gasa da wani ko wata.

Kwanan baya, cibiyar nazarin manufofin kasa da kasa ta Lowy dake kasar Australia ta fidda wani rahoto, inda ta bayyana cewa, sabo da karuwar kasashen da suka kulla dangantakar diflomasiyya da kasar Sin, a shekarar 2019, ya sa yawan ofisoshin jakadancin kasar dake ketare ya sha gaban na kasar Amurka. Wasu suna ganin cewa, saurin karuwar yawan ofisoshin jakadancin Sin a kasashen ketare ya nuna aniyar kasar Sin ta shiga harkokin kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China