Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala zabukan gundumomi a yankin Hong Kong
2019-11-25 19:42:51        cri
A yau da rana ne, aka kammala kidaye kuri'un zabukan gundumomi na wa'adi na 6 da aka gudanar a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin.

Su dai wadannan majalisu gundumomi dake matakin gunduma, su ne suke baiwa gwamnatin yankin musamman na Hong Kong shawara kan batutuwan da suka shafi rayuwar mazauna yankin da ma shiga ayyukan tafiyar da harkokin yankin.

A cikin sama da watanni biyar da suka gabata, tashin hankali, ta hanyar tsoma baki daga kasashen ketare, sun kara tsananta rikicin, lamarin da ya haifar da rudani a harkokin jin dadin jama'a da ma yin fito na fito a fannin siyasa, abin da ya kawo koma baya ga harkokin tattalin arziki da rayuwar jama'a. Watannin da yankin ya shafe yana fuskantar tashin hankali, ya dagula harkokin zabe matuka.

Ko da a ranar zaben, wasu masu tayar da bore sun yiwa 'yan takara barazana. Yanzu babban aikin dake gaban yankin na Hong Kong, shi ne kawo karshen tashin hankalin, tare da maido da doka da oda. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China