Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan sandan Hong Kong sun kama mutane 200 da kwace bama-baman fetur 188 a tarzomar ranar Asabar
2019-11-03 16:19:27        cri
Jami'an 'yan sandan yankin musamman na Hong Kong sun sanar a yau Lahadi cewa sun damke sama da mutane 200 wadanda ke da hannu wajen shirya gangami ba bisa ka'ida da haddasa tashe-tashen hankula a ranar Asabar din da ta gabata, kana sun kwace wasu makamai da suka hada da boma boman da ake hadawa da fetur kimanin 188.

A cewar sanarwar 'yan sandan, da misalin karfe 1 na safiyar yau Lahadi aka kama sama da mutane 200 wanda suka yi taron gangami da ya keta doka, suna dauke muggan makamai, sun aikata barna, kuma suna amfani da wasu abubuwan rufe fuskoki a lokacin da suka yi gangamin.

Mummunan tashin hankalin da kuma barnata kayayyakin da masu boren suka yi a yankin tsibirin Hong Kong da kuma Kowloon ya faru ne a sanadiyyar taron gangamin da suka shirya ba bisa ka'ida ba da yammacin ranar Asabar. Masu boren sun toshe hanyoyin wucewa, sun cinna wuta a wani shinge, kana suna dauke da boma bamai na fetur, sun yi ta jifan jami'an 'yan sanda.

'Yan sandan sun yi Allah wadai da babbar murya ga masu zanga zangar, da ta da hankali, da kuma lalata kayayyaki, wanda hakan ya saba doka da oda. Barnata kayayyakin da masu boren suka yi ya haifar da illa ga zaman rayuwar al'umma ta yau da kullum kuma ya saba doka da oda. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China