Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yunkurin da wasu kasashen waje ke yi na shiga harkokin cikin gidan Hong Kong ba zai nasara ba
2019-11-19 09:16:21        cri

Jaridar Peoples Daily ta kasar Sin ta rawaito a yau Talata cewa yunkurin da wasu kasashen waje ke yi na shiga harkokin Hong Kong ba za su taba samun nasara ba.

Jaridar ta yi tsokaci cewa, a lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping yake halartar taron kolin BRICs a kasar Brazil, ya gabatar da muhimmin jawabi game da halin da ake ciki a yankin musamman na Hongkong. Cikin jawabin nasa ya ce, gwamnatin kasar Sin a shirye take ta kalubalanci dukkan masu neman yin shisshigi daga ketare a harkokin cikin gidan Hongkong.

Bugu da kari, yaridar ta nanata cewa, wasu mutane da ake dauka a matsayin masu hikima suna tafkar babban kuskure ne, yunkurin da suke yi daga ketare na shiga harkokin Hong Kong ba kawai yana bayyana tsananin munafurcinsu game da kare hakkin dan adam da demokaradiyya ba ne, sai dai yana nunawa dukkan Sinawa ciki har da mutanen Hong Kong, don su gane ainihin siffarsu da manufar da suke da shi na nuna kiyayya ga kasar Sin da nuna kiyayya game da rikicin Hong Kong. Gwamnatin kasar Sin ba za ta taba lamintar yin katsa landan na wasu bangarorin waje don su cimma burinsu kan harkokin cikin gidan Hong Kong ba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China