Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Burin masu tsoma baki daga ketare cikin yankin Hong Kong ba zai cika ba
2019-11-19 09:28:01        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cikin jawabin da ya gabatar cewa, duk wata mummunar manufa ta hanyar tsoma baki cikin yankin Hong Kong na kasar Sin da wasu daga ketare ke yi, ba zai cimma nasara ba.

Shi ma wakilin yankin Port a majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin Cai Yi, ya bayyana cewa, matsayin shugaba Xi Jinping kan yanayin da ake ciki a yankin na Hong Kong, kamar yadda ya bayyana cikin jawabin da ya gabatar a kasar Brazil, ya bayyana yadda gwamnatin tsakiyar kasar ke dora muhimmanci da ma damuwa da halin da yankin na Hong Kong ya fada.

A hannu guda kuma, shugaba Xi ya aike da sako mai karfi na nuna goyon baya da kokarin da mahukuntan yankin ke yi na kawo karshe tashin hankali da rikicin dake faruwa. Wannan ya sanya mazauna yankin farin ciki, kan yadda babban yankin ke goyon bayan yankin musamman na Hong Kong, ba kuma wanda zai iya samun galaba ko raba shi daga kasar Sin.

Wani wakilin yankin Port a majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin, kana mamba majalisar zartarwas yankin musamman na Hong Kong Ye Guoqian, ya bayyana cewa, jawabin shugaba Xi Jinping, ya bayyana bukata karara kan nuna gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na nuna adawa da tashin hankali da rudanin dake faruwa

Ya ce, ya kamata gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, ta dauki wannan batu a matsayin jagora wajen sanya ido bisa doka don hukunta wadanda suka aikata laifi. Haka kuma, bai kamata jama'a su kuma gyefe guda ba, kamata ya yi su nuna cikakken goyon baya ga gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, su kuma hada kai wajen ganin an samar da kwanciyar hankali da makoma mai kyau a yankin. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China