Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakatare Janar na MDD ya yi kira da a taimakawa Afrika yaki da COVID-19
2020-05-20 14:06:18        cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga kasashen duniya su taimakawa nahiyar Afrika yaki da COVID-19.

Yayin wani sakon bidiyo game da kaddamar da bayani kan tasirin COVID-19 a Afrika, Antonio Guterres ya ce har yanzu cutar na matakan ta na farko a nahiyar, kuma akwai yiwuwar ta bazu cikin sauri. Ya na mai cewa ya zama wajibi kasashen duniya su taimakawa nahiyar tun yanzu domin ta samu farfadowa.

Ya kara da cewa, kawo karshen annobar a Afrika, na da muhimmanci wajen kawo karshenta a duniya baki daya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China