Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'ar MDD: Shirin raya tattalin arzikin Sin ya samar da abin koyi ga Afrika
2020-02-27 10:10:50        cri

Wata babbar jami'ar MDD ta ce, shirin raya tattalin arzikin da kasar Sin ta aiwatar da irin nasarorin da ta samu a shirinta na yaki da fatara sun samar da abin koyi ga kasashen Afrika a yayin da nahiyar ke kokarin cimma nasarar shirin samar da dawwamamman ci gaba na (SDGs).

A zantawarta da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a gefen taron shiyya na dandalin samar da dawwamamman ci gaba na Afrika karo na shida wanda ake gudanarwar a yankin Victoria Falls, na kasar Zimbabwe, sakatariyar hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD Vera Songwe, ta ce bunkasa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen Afrika ya kasance babban jigo wajen cimma nasarar shirin SDGs.

Songwe ta ce, bunkasa harkokin cinikayya na shiyya ya taka gagarumar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Sin, ta kara da cewa, huldar cinikayya a tsakanin kasashen Afrika tana da kyakkyawar makoma wajen bunkasa ci gaban tattalin arzikin nahiyar da ci gaban shiyyar.

Vera ta ce, gabanin kasar Sin ta fara fitar da kayayyakinta zuwa ketare, ta fara ne da huldar ciniki a shiyyar Asiya. Wato ta fara ne da kasuwanci a tsakanin kasashen gabashin Asiya, sai kuma ta shiga yammacin duniya da kasashen Turai da kuma Amurka.

Ta ce a halin da ake ciki yanzu kasuwancin da Afrika ke gudanarwa a cikin nahiyar kashi 17% ne. Yayin da gabashin Asiya ke gudanar da kasuwanci a shiyyarta da kashi 68%. Idan Afrika za ta gudanar da kasuwanci na kashi 68 a tsakanin nahiyar, za ta iya samar da guraben ayyukan yi, kana za ta iya samar da albarkatun da ake bukata wajen raya tattalin arzikin nahiyar cikin sauri kamar yadda kasar Sin ta yi.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China