Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi kira da a kaucewa kalaman kiyayya da kin jinin baki yayin tunawa da kisan kiyashin Rwanda
2020-04-08 11:12:58        cri

Sakatare Janar na MDD, Antonio Guterres, ya bukaci a kauracewa furta kalaman kiyayya da kin jinin baki, yayin da ake tunawa da ranar da aka fara kisan kiyashi a kasar Rwanda.

A cewarsa, dole a tabbatar da ba a sake samun faruwar lamarin ba. Kuma dole ne a kaucewa furta kalaman kiyayya da kin jinin baki, da gujewa abubuwan dake ingiza rarrabuwar kawuna da bambancin asali.

Kisan kiyashin Rwanda ya auku ne tsakanin ranar 7 ga watan Afrilu zuwa 15 ga watan Yulin 1994, inda aka kashe sama da mutane miliyan 1. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China