Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe jami'in kiyaye zaman lafiya na MDD a CAR
2020-03-17 14:59:06        cri

Kakakin MDD ya ce an hallaka wani dan kasar Burundi jami'in kiyaye zaman lafiya na MDD a lokacin da yake yunkurin dakile harin 'yan bindiga a jamhuriyar tsakiyar Afrika (CAR).

Shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a CAR (MINUSCA), Mankeur Ndiaye, ya yi Allah wadai da harin da aka kaddamar kan jami'in wanzar da zaman lafiyar, kana ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan jami'in wanzar da zaman lafiyar da kuma gwamnatin Burundi.

Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres, shi ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ake gudanarwa a ko wace rana.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China