Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin MDD: Somaliya na ci gaba na fuskantar kalubalen jin kai
2020-02-25 10:43:53        cri
Wakilin musamman na babban sakataren MDD a Somaliya James Swan, ya bayyana a jiya Litinin cewa, kasar Somaliya tana ci gaba da fuskantar matsanancin kalubalen jin kai.

James Swan wanda ya bayyana haka, yayin da yake yiwa kwamitin sulhun majalisar karin haske game da halin da ake ciki a kasar ta Somaliya, ya ce, kimanin mutane miliyan 5.2 ne a kasar suke bukatar taimako, biyo bayan matsalolin fari, ambaliyar ruwa da rikici da rashin tsaro da suka addabi kasar. A cewarsa, duk wadannan matsaloli kafin matsalar farin dango da kasar ta taba fuskanta a cikin shekaru 25.

Yana mai cewa, hukumar samar da abinci da aikin gona, tana taimakawa gwamnati shawo kan tasirin da wannan matsala za ta haifar kan samar da abinci. Don haka ya yi kira ga masu ba da gudummawa, da su hanzarta samar da taimakon kudi don taimakawa shirin kai daukin jin kai na shekarar 2020.

Ya ce, muddin ana son haka ta cimma ruwa na dogon lokaci, wajibi ne mu taimakawa shirin raya kasa na gwamnatin Somaliya, wajen cimma nasarar manufofin jin kai da gina kasa da tabbatar da zaman lafiya. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China