Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a yi muhawara game da tsaron Afirka yayin taron kwamitin tsaron MDD
2020-03-03 11:40:36        cri

Kwamitin tsaron MDD ya shirya gudanar da zaman muhawara game da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka a ranar 11 ga watan Maris din nan, taron da zai maida hankali ga batun yaki da talauci da tsattsauran ra'ayi.

Da yake yiwa manema labarai karin bayani game da ayyukan kwamitin na wannan wata, wakilin dindindin na kasar ta Sin a MDD, kuma shugaban zaman kwamitin na watan na Maris Zhang Jun, ya ce nahiyar Afirka na da damammakin samun ci gaba, amma kuma tana fuskantar tarin kalubale da rashin tabbas.

Zhang ya ce ya zanta da jakadun Afirka da dama, da wakilan musamman na babban magatakardar MDD game da kasashen nahiyar, wadanda kasashen suke fuskantar kalubalen ta'addanci iri daya da juna."

Ya ce "ta bakin babban magatakardar MDD, da wakilan kasashen Afirka, muna fatan za mu samu zarafin jin ta bakin juna kan al'amuran Afirka, musamman wajen samo hanyoyi na musamman, da dabarun shawo kan wadannan matsaloli dake barazana ga nahiyar Afirka". (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China