Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Sin na tsayawa tsayin daka wajen raya tattalin arziki mai bude kofa ga waje
2020-05-23 22:13:03        cri

Yayin da yake halartar cikakken zaman taron 'yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa mai kula da tattalin arziki ta kasar Sin, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, a halin yanzu, wasu kasashen duniya sun nuna ra'ayin kariyar ciniki, amma, kasar Sin tana tsayawa tsayin dake kan kare tsarin ciniki tsakanin kasa da kasa da kuma raya dangantakar dake tsakanin kasa da kasa bisa ra'ayin dimokuradiyya. A nan gaba kuma, za ta ci gaba da neman bunkasuwa bisa ka'idojin bude kofa ga waje, da hadin gwiwa da kuma cimma moriyar juna, domin inganta bunkasuwar tattalin arzikin duniya ta fuska mai bude kofa ga waje da fahimtar juna da cimma daidaito da kuma cimma moriyar juna, ta yadda za a gina tsarin tattalin arzikin duniya mai bude kofa ga waje.

A sa'i daya kuma, ya ce, kasar Sin za ta dukufa wajen kiyaye tsarin samar da kayayyaki, domin yin kandagarkin manyan kalubalolin da abin ya shafa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China