Da misalin karfe 3 na yammacin gobe Lahadi, za a shirya taron manema labarai a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing, inda wakilin majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, zai amsa tambayoyin 'yan jarida na kasar Sin da na kasashen ketare za su yi masa, game da batutuwan dake shafar manufofin diflomasiyyar Sin da kuma dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen ketare.
A lokacin kuma, sashen Hausa na babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) zai watsa labaran taron ta shafin intanet da shafinsa na FACEBOOK kai tsaye. (Maryam)