Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
XI: Ya kamata kamfanoni masu zaman kansu su samu ci gaba yayin da suke shawo kan matsaloli iri iri
2020-05-23 21:51:03        cri
Yau Asabar da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci cikakken zaman taron 'yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa sashen tattalin arziki ta kasar Sin, dake halartar taro na uku na majalissar CPPCC, inda ya saurari shawarwari daga wajensu.

A yayin taron, dan majalisar Liu Yonghao ya gabatar da jawabi game da kalubalolin dake gaban kamfanoni masu zaman kansu. Dangane da jawabinsa, Xi Jinping ya ce, a halin yanzu, kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin sun sami bunkasuwa matuka, sun kuma ba da babbar gudummawa wajen gina tsarin gurguzu irin na kasar Sin, yana mai cewa lallai sun yi babban aiki. Ya ce a nan gaba kuma, za a ci gaba da neman hanyoyin bunkasuwa, da dukufa wajen warware dukkanin matsalolin da za a gamu da su. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China