Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya halarci taron 'yan majalissar CPPCC masu kula da tattalin arziki
2020-05-23 15:28:00        cri
A yau Asabar, shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, mista Xi Jinping, ya halarci taron tattaunawar 'yan majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin CPPCC, masu kula da harkokin tattalin arziki, inda ya saurari shawarwarin da 'yan majalissar suka gabatar.

'Yan majalissar da suka halarci wannan taron sun hada da manyan jami'ai na sassan tattalin arziki, da shugabannin manyan kamfanoni da bankuna mallakar kasa, gami da shahararrun masanan ilimin tattalin arziki. Yadda shugaba Xi Jinping ke musayar ra'ayi da su, ya janyo hankali sosai, bisa la'akari da yanayin da ake ciki na fama da matsin lamba a fannin tattalin arziki, sakamakon annobar COVID-19. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China