Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Samun goyon baya daga jama'a shi ne tushen mulki ga JKS
2020-05-22 21:04:47        cri
A yau Juma'a, shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), kana shugaban hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar Xi Jinping, ya halarci shawarwarin da wakilan yankin Mongolia ta gida suka gudanar, a zaman taro karo na 3 na majalissar wakilan jama'ar kasar Sin ta 13.

Yayin zaman, shugaban ya ce samun goyon baya daga jama'a shi ne tushen mulkin JKS. A cewarsa, tsarin dimokuradiya mai salon tsarin gurguzu na kasar Sin, wani ingantaccen tsari ne mai matukar amfani a fannin kare moriyar jama'a. Don haka dole a tsaya kan wannan tsari na dimokuradiya, don samun hadin gwiwar jama'a, musamman ma a fannin dabaru da karfin aiwatar da ayyuka.

Ban da haka, shugaban na Sin, ya jaddada muhimmancin samar da wasu managartan matakai, na gudanar da wasu manyan ayyuka, da kula da kananan wurare daban daban yadda ake bukata. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China