Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta iya warware matsalolin da take gamuwa da su ta fuskar tattalin arziki
2020-05-22 19:15:49        cri
Da safiyar yau Jumma'a ne shugaban kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin, He Lifeng, ya bayyana cewa, ko da yake, barkewar cutar numfashi ta COVID-19 ya haddasa asara ga tattalin arzikin kasar Sin, amma a halin yanzu, tattalin arzikin kasar yana farfadowa cikin sauri.

Ya ce, ayyukan gona suna ci gaba da bunkasa cikin yanayi mai kyau, sa'an nan, harkokin masana'antu su ma suna bunkasa yadda ya kamata, musamman ma ta fuskar masana'antun zamani. Kaza lika masana'antun gargajiya ma suna farfadowa cikin sauri.

He ya ce bullar cutar COVID-19 ta haddasa asarar ayyukan ba da hidima sosai, amma, sannu a hankali, ana samun farfadowar ayyuka masu nasaba da hakan.

He Lifeng ya kara da cewa, bisa hasashen da aka yi, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da bunkasuwa cikin yanani mai kyau. Kuma kasar Sin tana da imani, kuma tana da karfi na tabbatar da dauwamammen ci gaban tattalin arzikin ta yadda ya kamata. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China