Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan sha'anin gona da kauyuka na kasar Sin: ba za a samu karancin hatsi a kasar Sin ba
2020-05-22 15:32:25        cri

Yau Juma'a, a gun taron manema labarai karo na farko na taro karo na 3 na NPC na 13, ministan sha'anin gona da kauyuka na kasar Sin Han Changbin ya nuna cewa, yawan hatsi da Sin ke samarwa ya haura ton miliyan 650 a ko wace shekara a cikin shekaru biyar da suka gabata a jere, yawan hatsin da ko wane mutum ya samu ya kai sama da ma'aunin da aka kayyade a duniya, abin da ya nuna cewa, ba za a samu karancin hatsi a nan kasar Sin ba ko kadan.

Ban da wannan kuma, Han ya ce, a shekarar bana an dauki wasu matakai da ba a taba ganin irinsu ba, don ba da tabbaci ga samar da isashen hatsi, matakin da ya tabbatar da kandagarkin cuta da kuma ayyukan shuke-shuke a lokacin bazara. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China