Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana da tabbacin cimma nasarar manufofinta na raya kasa na shekarar 2020
2020-05-22 11:11:22        cri

Kasar Sin ta bayyana kudurinta na zage damtse don tabbatar da ganin ta cimma nasarar manufofinta na raya kasa game da kawar da talauci da kammala gina al'umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni a wannan shekara, duk da cewa ba ta ayyana wani mizanin ci gaban tattalin arzikin da take fatan cimmawa a shekarar ta 2020 ba.

Wannan na kunshe ne cikin rahoton aikin gwamnati da aka gabatarwa majalisar wakilan jama'ar kasar don tattaunawa.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, an yanke shawarar jingine hakikanin mizanin ci gaban tattalin arzikin da ake fatan samu ne, saboda wasu matsaloli na bazata da kasar ka iya fuskanta yayin da take aiwatar da matakanta na raya kasa, biyo bayan wasu abubuwa na rashin tabbas da ka iya kunno kai dangane da COVID-19, da yanayin tattalin arzikin duniya, da harkokin cinikayya.

A don haka rahoton ya ce, wajibi ne a mayar da hankali kan fannoni 6, don tabbatar da nasarar sassa guda shida. Yin haka zai taimaka wajen bunkasa ginshikan daidaita tattalin arzikin kasar. Kula da bangaren tsaro, zai samar da kwanciyar hankanlin da ake bukata na samun ci gaba, matakin da zai samar da ginshikin cimma nasarar manufofin da kasar ta sanya a gaba na gina al'umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni.

Kasar Sin za ta dora muhimmanci wajen daidaita batun samar da ayyukan yi da inganta rayuwar jama'a, da yin bayani dalla-dalla kan burin da ake fatan cimmawa, da manufofi da kuma matakai.

Bugu da kari, a wannan shekara, kasar Sin tana fatan kara samar da sabbin guraben ayyukan yi sama da miliyan 9 a biranen kasar da sanya ido wajen rage adadin marasa ayyukan yi a birane zuwa a kalla kaso 6 cikin 100. Daga karshe rahoton, ya ce, kasar Sin za ta tsame dukkan mazauna

Karkara da ma yankuna masu fama da talauci na kasar dake rayuwa a kasa da mizanin talauci daga kangin talauci.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China