Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kara rage sassan da aka haramta zuba jari ga masu jarin waje
2020-05-22 11:16:16        cri

Kasar Sin za ta kara rage sassan da a baya aka haramtawa masu jarin waje zuba jari a cikinsu, kamar yadda aka bayyana cikin rahoton aikin gwamnati da aka gabatarwa zaman majalisar wakilan jama'ar kasar da aka bude Jumma'r nan domin ta tattauna a kai.

Haka kuma, kasar Sin za ta kafa sabbin yankunan cinikayya maras shige na gwaji (FTZs) da yankunan adawa da samar da kayayyaki a yankunan tsakiya da yammacin kasar, da kare tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, baya ga shiga a dama da ita wajen yiwa kungiyar cinikayya ta duniya gyaran fuska.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, kasar Sin ta jaddada muhimmancin aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya da aka cimma tsakanin Sin da Amurka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China