Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cutar COVID-19 Ta Sa An Gano Karyar Da Amurka Ta Yi Cewar, Wai Akwai Daidaito Tsakanin Dukkan Al'ummomi
2020-05-23 20:43:16        cri
A ranar 21 ga wata, Asusun kula da yara na MDD ya gargadi Amurka cewa, dole ne ta tsayar da korar yara zuwa kasashen ketare, musamman ma wadanda ba su da iyalai. Lamarin da ya nuna tabarbarewar yanayin hakkin dan Adam a kasar Amurka bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19.

Daga farkon watan Maris na bana, ya zuwa yanzu, gaba daya gwamnatin kasar Amurka ta kori yara a kalla dubu 1 zuwa kasashen Mexico, El Salvador, Guatemala da Honduras, kuma ba wanda ke raka su. Kuma wasu sun kusan rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da cutar COVID-19 da rashin wuraren kwana.

Haka zalika kuma, wasu jihohin kasar Amurka sun taba ba da umurni ga hukumomin kula da tsoffafi don su samar da gadaje ga masu kamuwa da cutar, wadanda suke warkewa sannu a hankali, kuma wadannan hukumomi ba za su iya nuna adawa da wannan umurni ba. Har ma, mataimakin gwamnan jihar Texas Dan Patrick ya taba yin kira ga tsoffafi da su sadaukar da kansu, maganar ta bata ran al'umma kwarai da gaske. Kana, bisa kididdigar da jaridar New York Times ta yi, 11% cikin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 sun zo ne daga hukumomin kula da tsoffafi, kuma kashi 1 bisa 3 cikin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon cutar suna da nasaba da gidajen kula da tsoffafi.

A hakika dai, matsalolin da tsoffafi, da yara, da masu fama da talauci suke fuskanta a lokacin annobar, ya kasance matsalolin da suka dade suna kasancewa a kasar Amurka, ya nuna ra'ayin wariyar launin fata, bambancin matsayi tsakanin masu arziki da talakawa da wasu harkoki rashin adalci da ake gamuwa da su cikin kasar Amurka. Kana, sabo da wasu matakan da 'yan siyasar kasar Amurka suka dauka a 'yan shekarun nan, ana ci gaba da fama da yanayin rashin adalci cikin wannan kasa.

Kamar yadda mujallar Times Weekly ta bayyana a ranar 20 ga wata, cewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta shaida yadda dimokuradiyya ta ci tura a kasar Amurka. (Mai Fassarawa: Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China