Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gyara Alkaluman Rasuwar Mutane, Ya Nuna 'Yan Siyasar Amurka Sun Fadi Jarrabawar Yaki Da Cutar COVID-19
2020-05-22 20:11:25        cri

Kwanan baya, kafar yada labaran siyasa ta "The Daily Beast" dake kasar Amurka, ta fidda labari dake cewa, shugabannin kasar Amurka, da tawaga mai gudanar da aikin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 ta gwamnatin kasar, suna matsa wa cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar lamba, don ta yi hadin gwiwa da jihohin kasar, wajen gyara yadda suke gudanar da ayyukan kididdigar yawan rasuwar mutane sanadiyar cutar COVID-19. Hakan dai ya sa alkaluman yawan rasuwar mutane daga jihohi da dama na kasar Amurkan da aka gabatar kwanan baya, suka yi kasa da hakikanin gaskiya.

Haka kuma, jaridar "The Hill" ta fidda labari dake cewa, ma'aikatar harkokin kiwon lafiyar jama'a da muhalli ta jihar Colorado, ta canja hanyar kididdigar yawan rasuwar mutane sanadiyyar cutar numfashi ta COVID-19.

Dangane da wannan batu, babban jami'in likitanci na ma'aikatar Eric France, ya yi bayani cewa, rahotannin da jihar ta gabatar a baya, game da rasuwar mutane sanadiyyar cutar, suna kunshe da wasu mutanen da suka rasu sakamakon wasu cututtuka da ba su da nasaba kai tsaye da COVID-19.

Kaza lika, bayanin nasa, ya yi daidai da yadda gwamnatin kasar Amurka ta yi nata bayanin kan wannan batu, lamarin da ya nuna cewa, gwamnatin kasar Amurka ta riga ta sanya hannu cikin harkokin likitancin kasar.

A halin yanzu, Ana dab da babban zaben kasar Amurka, amma wasu 'yan siyasan kasar sun ki karbar shawarar jami'an lafiya, inda maimakon haka, suke kara matsa wa jihohin kasar lamba, don su gyara alkaluman yawan rasuwar mutane, matakin da ke matukar bakanta ran al'ummar kasar!

Shi ya sa, a ranar 21 ga wata, kamfanin dillancin labarai na CNN ya ruwaito rahoton cibiyar nazarin cututtuka masu yaduwa ta jami'ar Minnesota cewa, alkaluman da gwamnatin kasar ta fidda game da cutar numfashi ta COVID-19 ba za su iya kasance dalili kan ko za mu iya dawo bakin aiki, ko a'a ba.

Cikin rahoton din, an ce, gwamnati da jihohin kasar ba su gudanar da cikakken bincike ba, kuma shugaban cibiyar Mike Osterholm ya bayyana cewa, yadda kasar Amurka take gudanar da bincike kan annobar ba shi da inganci ko kadan!

Dukkanin matakai na rashin hankali da 'yan siyasan kasar Amurka suke dauka, za su shigar da al'ummomin kasar cikin mawuyacin hali, har ta kai a samu karin rasuwar mutane a kasar. Kamar yadda masanin kiwon lafiyar jama'a na jami'ar Columbia Lucky Tran ya bayyana, "A lokacin da 'yan siyasa suke sa ido kan masana kimiyya da fasaha, da kuma wasa da alkaluma, mu ne za mu sha wahala." (Mai Fassarawa: Maryam Yamg)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China