2020-05-19 20:50:10 cri |
Bayan shiga watan Mayu, yanayin yaduwar cutar COVID-19 na kara tsananta a kasar Amurka, lamarin da ya sa wasu 'yan siyasan kasar ke ci gaba da kokarin dorawa kasar Sin laifi, tare da haifar mata da matsala. Don haka ne kuma suka tsara batun "gayyato yankin Taiwan don ya halarci taron hukumar WHO". Inda majalisar gudanarwar kasar Amurka ta nuna goyon baya ga yankin na Taiwan, a shafin sada zumunta na Twitter, sa'an nan majalissun kasar suka yi kira ga gwamnatocin kasashe kimanin 60, da su nuna goyon baya ga Taiwan, har ma majalissar datawan kasar ta zartas da wani kuduri, na sanya sakataren harkokin wajen kasar ya tsara wata dabara, ta taimakawa yankin Taiwan samun matsayi na mai sa ido a cikin hukumar WHO.
Amma hakika su ma wadannan 'yan siyasa na kasar Amurka, sun san cewa, dole ne za su ci tura, duba da cewa, suna neman kalubalantar manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. Don gane da wannan batu, Steven Solomon, jami'i mai kula da batun shari'a na hukumar WHO, ya jaddada a kwanan baya cewa, jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ita ce wakiliyar al'ummar Sin daya tak, dake da matsayi na halas cikin tsarin MDD, kuma hukumar WHO za ta dauki mataki iri daya da na MDD. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China