Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko 'Yan Siyasan Amurka Suna Son A Kira Su "Sarakuna Masu Dora Laifinsu Kan Saura"
2020-05-20 21:22:15        cri
A ranar 18 ga wata, Shugaban kasar Amurka, ya gabatar da wasikar da ya aike ga babban sakataren hukumar kiwon lafiyar duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus, inda ya tilastawa hukumar da ta yi kwaskwarima cikin kwanaki 30. Ya ce, in ba haka ba, kasar Amurka za ta dakatar da samar mata kudade, za ta kuma janye jikinta daga hukumar.

Bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19 cikin kasa da kasa, 'yan siyasar gwamnatin kasar Amurka, sun gaza aiwatar da aikin dalike yaduwar cutar yadda ya kamata, don haka suka dukufa wajen dora laifinsu kan kasar Sin. Da hukumar WHO, da kungiyar tarayyar kasashen Turai, da kuma abokan adawarsu na cikin Amurka.

Amma kuma, dukkanin karyar da suke yadawa, ba za su iya boye kuskuren da suka yi game da aikin dakile yaduwar annobar ba, kamar yadda kafofin watsa labaran kasar suka bayyana. Inda suka ce 'yan siyasar ba su lura da gargadin da kasar Sin, da ma sauran bangarori suka fidda ba, kuma sabo da wannan laifi na su, mutane sama da miliyan 1.52 suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19, yayin da kuma cutar ta hallaka mutane sama da dubu 91.

Amma, a nasu bangare, babban magatakardan MDD, da shugabannin kasashe da dama da suka hada da na kasar Jamus, da na kasar Faransa da sauransu, sun jaddada goyon bayansu ga hukumar WHO, yayin babban taron kiwon lafiyar na duniya. Sun kuma nuna cewa, yanzu lokaci ne na hadin gwiwa, bai kamata a yi ta zargin wani bangare ba, ko kuma bata hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban.

Tsohon shugaban kasar Amurka Harry Truman, ya taba bayyana cewa, "A dauki nauyi, kada a dora shi kan wasu". Muna fatan 'yan siyasan kasar Amurka za su maimaita wannan magana, su gyara kuskurensu cikin sauri, su kuma hada kai da kasa da kasa, domin ceto al'ummomin kasar Amurka, wadanda suke fama da matsalar yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China