Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko Shakka Babu 'Yan Siyasan Kasar Amurka Dake Wasa Da Ra'ayin Wariyar Launin Fata Za Su Ci Zarafin Kansu
2020-05-18 21:27:21        cri

Kwanan baya, magajin garin birnin San Antonio na jihar Texas dake kasar Amurka Ron Nirenberg ya nuna damuwarsa kan karuwar ra'ayoyin wariyar launin fata, domin magance yaduwar wadannan ra'ayoyi, 'yan majalisar dokikin birnin, sun zartas da kudurin daina yin amfani da kalmar "kwayar cutar Sin" ko "kwayar cutar Kongfu" da dai sauran kalmomin dake cin zarafin wata kalibar musamman, ko kuma al'ummomin wani yankin musamman.

Bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Amurka, wasu 'yan siyasan gwamnatin kasar sun dukufa, wajen dora laifinsu kan sauran mutane, domin dauke hankulan al'ummomin kasar daga kasawarsu, ta yaki da cutar.

Ministan harkokin wajen kasar Mike Pompeo, ya rika yin hakan sau da dama, ya kuma taba kiran cutar numfashi ta COVID-19 "cutar Wuhan", har ma ya yi yunkurin yada wannan ra'ayi nasa a dandalin kasa da kasa.

Sakamakon bullar wannan ra'ayi da suka nuna bayan barkewar annobar, an rika fama da karin matsaloli ta fuskar nuna wariyar launin fata a kasar Amurka.

Bisa binciken da jaridar The Washington Post ta yi, bayan barkewar annobar, adadin rashin aikin yi na al'ummar Latin Amurka, da na al'ummar Afirka dake Amurka ya haura zuwa 20% da 16%. Kana, adadin rashin aikin yi na farin fata ya kasance kaso 11%, lamarin da ya bata ran kanannan kalibu na kasar Amurka kwarai da gaske.

A ganin wadannan 'yan siyasan kasar Amurka, mai yiwuwa ne a cimma moriya bisa rabuwar al'ummar kasa. A hakika dai, sun shigar da al'ummar kasa cikin kiyayya, lamarin da zai haddasa babbar hasara gare su. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China